Kamfanin dillancin labarai na kasa da kasa na Ahlulbayt (As) –ABNA- ya habarta cewa: Kungiyar Mujahidan Palastinu ta tabbatar da shahadar wanda ya assasa kuma babban sakataren kungiyar Asaad Abu Sharia (Abul-Sheikh) a cikin wata sanarwa.
Bayanin ya ci gaba da cewa: Sheikh Asaad Atiyah Abu Sharia (Abul-Sheikh) malamin addinin musulunci kuma kwamandan mujahidai daga rukunan jihadi da gwagwarmayar Palastinu, wanda shi ne babban sakataren kungiyar kuma kwamandan rundunar soji ta kungiyar Mujahidin ya yi shahada a harin bam da aka kai a unguwar Sabra da ke birnin Gaza a ranar Asabar din da ta gabata.
A wannan harin bam din, Ahmed Atiyah Abu Sharia (Abul-Falsetin) dan uwa ga Sakatare Janar kuma memba a Sakatariyar Harkar Mujahidin kuma shugaban kungiyar reshen Gaza, da wasu da dama daga cikin iyalan Abu Shari'a sun yi shahada.
Your Comment